Yan bindiga sun hallaka jami’an hukumar tsaro ta (NSCDC) 8

FB IMG 1757235242128

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun hallaka jami’ai takwas na Hukumar Tsaro ta Fararen Hula (NSCDC) da ke aiki a kamfanin siminti na BUA Cement da ke Okpella, karamar hukumar Etsako East ta jihar Edo.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 5 ga Agusta, 2025, misalin ƙarfe 10 na dare, lokacin da jami’an suka fita raka wasu ma’aikatan kamfanin ’yan ƙasar China guda biyar bayan kammala aikin gadi a ƙofar kamfanin.

Wani babban jami’in rundunar a jihar ne ya bayyana haka a ranar Asabar, inda ya ce ’yan bindigar sun hallaka jami’an tare da jikkata huɗu waɗanda ke karɓar magani a asibiti a halin yanzu.

Aminiya

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *