Alfijr
Alfijr ta rawaito a daren Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a Cibiyar gyaran hali da tarbiyya ta Kuje da ke Abuja, babban birnin kasar da bama-bamai.
Harin ya zo ne a wani mataki da ake ganin sun dauka na shiga ginin tare da ‘yanto wasu daga cikin mambobinta.
Alfijr
An kai hari gidan yarin da misalin karfe 10:27 na dare. tare da bama-bamai da harbin bindiga.
Bincike ya nuna cewa ’yan bindigar da ake zargin sun kai hari ne a bayan harabar.
Fashewar da karar harbe-harbe ya jefa yankin cikin rudani da firgici yayin da mazauna yankin suka yi ta tururuwa domin tsira da rayukansu.
A halin da ake ciki dai har yanzu mahukunta ba su mayar da martani kan lamarin ba
Alfijr
Karin Bayani na nan tafe