Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7, Sun Harbi Daya A Babban Birnin Najeriya Abuja

Screenshot 20221027 112452 com.android.chrome edit 10136481627099

An sace mutanen yayin jama’a suka shiga sallar magariba a masallaci.

Alfijir labarai ta rawaito wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da akalla mutum bakwai a kauyen Igu da ke yankin Sherefe a Karamar Hukumar Bwari ta babban birnin tarayya.

Lamarin ya faru ne da daren ranar Alhamis din da ta gabata.

Wani mazaunin yankin, Muhammad Yahaya, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun isa unguwar ne a lokacin da mutane suka shiga masallaci domin yin sallar magariba.

Yahaya ya ce an yi awon gaba da mutum bakwai, sannan maharan sun harbi mutum daya da bindiga.

Lamarin na zuwa ne mako guda bayan da aka sace wani hakimin yankin, Chebawaza Sariki, amma daga baya aka sako shi a daren Asabar.

Haka kuma, kimanin wata guda, an sace mutum biyu a wasu yankuna biyu na Sherefe.

A baya-bayan nan hare-haren yan bindiga na ci gaba da kamari a wasu yankunan birnin tarayya, Abuja.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *