Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce riKicin siyasar ƙasar Nijar haɗi da takunkuman da aka ƙaƙaba mata sakamakon juyin mulki ya jefa ɗimbin jama’ar ƙasar da ke yankin Sahel cikin “uƙuba”.
Alfijir Labarai ta rawaito a watan da ya gabata kaɗai an samu ƙaruwar rikici da tashe-tashen hankali da suka kai ga raba kimanin mutum 20,000 daga muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata.
Wannan ya haifar da cikas wajen samar da cikakkiyar kariya ga ‘yan gudun hijira da masu neman mafaka har ma da waɗanda ke ba su mafakar.
Hukumar lura da ƙaurar jama’a da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗunkin Duniya, UNHCR, ta ce ta shaida ƙaruwar matsaloli da kashi 50 cikin 100 da suka haɗa da satar jama’a domin neman kuɗin fansa da rikicin cikin gida a kwana biyar da yin juyin mulkin a watan da ya gabata.
“Dambarwar siyasa da ke ci gaba da faruwa da kuma rashin alamun sasantawa a kusa na ci gaba da haifar da barazana lura da yadda ake yawan samun yawaitar hare-hare daga ƙungiyoyi masu ɗaukar makamai, musamman a kan iyakokin ƙasashen Mali da Burkina Faso”, kamar yadda jakadan UNHCR a Nijar ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva.
Hukumar ta ce waɗanda rikicin ya shafa sun haɗa da ‘yan Nijar 350,000, waɗanda tun asali rikicin cikin gida ya ɗaiɗaita su.
Akwai irin wannan adadin na masu neman mafaka da baƙi ‘yan gudun hijira da suka fito daga maƙwabtan ƙasashe.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
Ba gaskiya bane mu mutanan Niger
Alhamdullilah
Shiga uku so uku yana Nigeria Malan dan jarida