‘Yanbindiga Sun Sace Malamin Zabe A Maradun

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Alfijr ta rawaito wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in zabe, mai suna Bashir shagari mai kula da karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Wata majiya ta shaidawa wakilinmu cewa Shagari yana Kan hanyarsa ne zuwa cibiyar tattara sakamakon zabe ta jiha (INEC) dake Gusau domin gabatar da sakamakon zaben gwamnan na karamar hukumar Maradun a lokacin da aka yi garkuwa da shi .

An bayyana cewa, wasu jami’in zaben na tare da wanda aka sa ce tare da wasu ma’aikatan INEC aka tare su a kan wata gada da ke kusa da garin Maradun.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar PUNCH, jami’in hulda da jama’a na hukumar INEC ta jihar, Muktari Janyau ya ce sun kai rahoton lamarin ga shalkwatar ‘yan sanda ta Jihar zamfara.

Ya kara da cewa “Kwamishanan zabe mai kula da jihar Zamfara, Farfesa Sa,idu Babura Ahmed ya kai rahoton lamarin ga kwamishinan ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace.

Zuwa lokacin hada wannan ruhoton mun Yi kokarin jin tabakin Hukumar ‘yansanda ta bakin jami’in hurda da jama’a na rndunar SP Mohammed Shehu Amma abinnyaci tura.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *