Yunƙurin juyin mulki: Ana musayar wuta a ƙasar Guinea

IMG 20231105 WA0004

Rahotanni daga ƙasar Guinea na nuni da cewa, ana zargin yunƙurin juyin mulki a ƙasar bayan da aka jiyo musayar wuta a Conakry, babban birnin ƙasar, a ranar Asabar.

Alfijir Labarai ta rawaito Shaidu sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, jami’an tsaro sun yi wa yankin ƙawanya, ba shiga ba fita.

Wata majiya da aka sakaya sunanta ta ce, “Ana musayar wuta daga tsakanin ɓangarorin da lamarin ya shafa tare da harba makaman yaƙi a Kaloum.”

“Tun da asuba aka kulle garin, ba shiga, ba fita,” in ji wani ɗan kasuwa a yankin.

Guinea na ɗaya daga jerin ƙasashen da suka fuskanci juyin mulki tun 2020. Sauran ƙasashen sun haɗa da Mali, Burkina Faso, Nijar da kuma Gabon.

Shugaban sojojin juyin mulki a Guinea, Kanal Mamady Doumbouya, ya karɓe ragamar shugabancin ƙasar ne a ranar 11 ga Satumban 2021 bayan da ƙasar ta shafe shekara 11 kan tarbar mulkin farar hula.

Inda Ranka

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *