Yunkurin Juyin Mulki A Burkina Faso Ya Gamu Da Tasgaro

sun dauki lokaci suna bibiyar Traore a gidansa da duk wuraren da ya je, haka kuma suke bibiyar makusantasu.

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin sojin Burkina Faso ta sanar da kame wasu sojoji kan zargin su da Yunƙurin kifar da gwamnatin Kyaftin Ibrahim Traore

Ofishin babban mai shigar da kara na kasar ya ce sojojin na fuskantar zargin zagon kasa ga gwamnatin Traore da yunkurin juyin mulki.

Sauran zarge-zargen sun hada da na karya dokokin soja da barazana da tsaron kasa da kuma yunkuri jefa rayuwar jama’a cikin hadari.

Ofishin ya ce duk sojojin da ake zargin biyu daga cikinsu na bakin aiki, na ukun ya yi ritaya.

Ya ƙara da cewa sun dauki lokaci suna bibiyar Traore a gidansa da duk wuraren da ya je, haka kuma suke bibiyar makusantansa.

Sanarwar gwamntin ta ce bayan dogon bincike ne aka kame su don amsa tambayoyi domin gano iyayen gidansu.

Ofishin na zargin su da yunkuri na wargaza gwamnatin rikon kwaryar da ke fatan dakile matsalolin tsaron da kasar ke fama da su.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *