Zabe: Kotun Daukaka Kara Ta Sake Korar Ƴan Majalisa Guda Uku

Shari'ar Zabe

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta kori ‘yan majalisar dokokin jihar Filato uku.

Alfijir Labarai ta rawaito an yanke hukuncin ne a ranar Lahadi, 19 ga Nuwamba, 2023, a ranar da kotun daukaka kara ta kori Gwamna Caleb Mutfwang.

Kwamitin alkalan kotun da mai shari’a Williams-Dawodu ya jagoranta, a wani hukunci na bai daya, sun kori Hon. Happiness Akawu, na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), inda ta bawa Hon. Yakubu Sanda na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), don wakiltar mazabar jihar Pengana.

Kotun ta kara korar Hon. Agbalak Adukuchill Ibrahim na PDP, da kuma Eli Bako Ankala na APC, ya wakilci mazabar Rukuba/Irigwe.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Hakazalika kotun ta kori Hon. Rimvjat Nanbol na PDP, inda ta bawa Hon. Daniel Ninbol Listic na Labour Party (LP) don wakiltar Langtang North Central, jihar mazabar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *