Shugaban hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da Rashawa ta jihar Kano Batista Muhyi Magaji Rimin Gado zai fara Kai ziyara runbunan ajiyar Kayan Abinci a Kano Dan fito da abincin da aka boye a sayarwa da jama’a.
Alfijir labarai ta rawaito Barista Muhyi Magaji Rimin Gado yace Haramin ne Kuma karya dokar kasa ne boye abinci Lokacin da ake tsanananin wahalar abinci a kasa .
Wakilinmu Tukur S Tukur ya rawaito mana cewa Za’a fara Kai simanen Wuraren da ake zargi an boye kayan Abinci ne kafin watan Azumin Ramadan.
Muhyi Magaji Rimin Gado yace wajen da zasu fara Dira shine Kasuwar Dawanau inda yace duk Wanda aka kama ya boye abinci za’a fito da abincin a kaishi kasuwa ,wanda hakan Zai taimaka wajen sauko da farashin kayan Abinci.
Rimin Gado yace dokar kasa ta bashi dama kodai ya fitar da kayan da aka boye zuwa kasuwa a sayar dasu ko ya kulle Rumbun ajiyar Kayan Abincin ya tafi Kotu
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V