Zamu Dawo Da Tashar, PYRAMID FM, Cikin Hayyacinta – Gwamnatin Kano

Aminu Bala Madobi.

A kokarin da take na sake farfado da tashar don cigaba da watsa shirye shirye bayan kwashe tsawon lokaci cikin mashasshara…

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin Kano ta bayyana shirin ta na kulla alaka da gwamnatin tarayya domin sake dawo da ci gaba da watsa shirye shirye da kuma magance katsewar shirye shiryen da tashar keyi.

Hon. Sulaiman Mukhtar, Dan majalisar dokokin Kano mai wakiltar Madobi ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ba zata da yakai babbar tashar dake kan titin yako, a Madobi.

Mukhtar ya nanata kudirin gwamnatin jihar Kano na samar da kayan zamani dan inganta tashar a kokarin dawo da ita cikin hayyacin ta, la’akari da muhimmancin ta ga al’ummar kanawa.

“Ba kamar yadda nakeji ba, ya zama wajibi na godewa Manajan tashar bisa jajircewar sa a kokarin maido da tashar ci gaba da watsa shirye shirye”

Daganan Dan majalisar ya bada tabbacin cewa an kammala dukkan shirin da ya dace domin yiwa tashar garambawul ta hanyar maido da farin jinin tashar tare da shaharar ta wajan nisan zango a arewacin Najeriya.

Tun da farko da yake maida jawabi, Manajan tashar Kwamaret Abba Bashir ya godewa Dan majalisar a madadin gwamnatin Kano bisa kawo daukin gaggawa duk da halin matsin tattalin arziki da ake ciki.

“Wannan ziyara, ita ce irin ta ta farko a tarihi tun bayan zamowa ta Manaja, ba wani jami’in gwamnati da ya taba kawo mini makamanciyar irin wannan ziyara”

Kwamaret yace a ƙarƙashin kulawar sa, zai yi dukkan mai yiwuwa don ganin wannan mataki ya tabbata ba tare da tangarda ba.

Gidan rediyon na tarayya , an samar da shi aranar 19 ga watan Maris 2004, zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar Kano Injiya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso a kokarin sa na sadar da al’ummar karkara da ababen more rayuwa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *