Zamu Hada Hannu Da Masu Sana ar Aiki Da Aljanu (‘YAN BORI) A Kano – In Ji El Mustapha

FB IMG 1718106581562

Daga Aminu Bala Madobi

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jahar Kano karkashin jagoranci Abba El-mustapha ta bata tabbacin hada hannu da masu Sana’ar aiki da Aljanu na jahar Kano (‘yan bori) domin tsaftace aiyukan su ta yadda zasu zama sunyi daide da ka’idar da doka ta tanadar musu.

Alfijir labarai ta ruwaito Abba El-mustapha na bayyana hakan ne a jiya yayin da ya karbi bakuncin shuwagabannin Kungiyar reshen jahar Kano a ofishin.

El-mustapha ya nemi hadin kan Kungiyar tare da cikakken goyan bayan su ta yadda za’a gudu tare a kuma tsira tare.

Dake jawabi amadadin kungiyar Mal. Sabo isyaku wailari, wanda shi ne Shugaban majalisar yan bori masu aiki da aljanu na karamar Hukumar kumbotso cewa yayi sun kawo ziyarar ga Hukumar tace fina-finai ne domin kulla alakar aiki ta bangaren da aikinsu ya hadu musamman tallata maganin gargajiya domin su tabbatar da ‘ya’yan Kungiyar su na yin amfani da kalmomin daba su ci karo da ka’idar dokokin Hukumar ba.

Haka kuma ya Kara da cewa Kungiyar na iya kokarin ta na tabbatar da ba suyi wasa a lokacin daya ci karo da lokacin sallah ba tare da kauracewa yin wasa a kusa da masallaci, makabarta ko makaranta.

A karshe ya yiwa Shugaban Hukumar Abba El-mustapha da ma’aikatan sa godiya a madadin ‘yan Kungiyar ‘yan bori ta jahar Kano baki daya dangane da irin tarbar da a ka yi musu cikin girmamawa. Mal. Sabo ya kuma yi alkawarin cewa Kungiyar su zata cigaba da bawa Hukumar cikakken hadin Kai tare da goyan baya.

Sanarwa daga:
Abdullahi Sani Sulaiman jami’in Hulda da jama’a na Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jahar Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *