Kotu ta Hana Hukamar EFCC Kamawa Da Tsare Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

FB IMG 1717093859719

Wata babbar kotun Kano da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako ta bayar da umarnin hana Hukumar  EFCC kamawa, tsarewa, tsangwama, tsoratarwa ko gayyatar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023 Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutane bakwai.

Alfijir labarai ta ruwaito mai shari’a Yusuf Ubale Muhammad ya bayar da wannan umarni ne na wucin gadi a ranar 5 ga watan Yuni, 2024.

“An ba da umarnin wucin gadine ga wanda ake kara da kada ya sake ko shi ko wakilansa, abokan hulda, ko duk wanda ke yin aiki a madadinsa, daga kamawa, tsarewa, tsangwama, tsoratarwa, ko gayyatar, mai kara har sai an saurari karar da masu kara suka shigar.

“Ya kuma ba da umarnin cewa duka umarnin wucin gadi da aka bayar, a tabbatar a baiwa wadanda ake kara kafin ranar da aka sanya don sauraron karar,” in ji alkalin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *