Zanga-zanga! Rundunar Yan Sandan Kano Ta Yi Karin Haske Akan Abun Da Ya Faru A Unguwar Kurna

FB IMG 1720352304988

Rundunar yan sandan jihar kano ta bayyana cewa al’ummar unguwar yankin unguwar kurna da Rijiyar Lemo ne suka fara afkawa Ofishin yan sanda na yankin a kokarinsu na dole sai sun cigaba da zanga-zanga duk da dokar hana fita da aka sanya.

Alfijir labarai ta ruwaito SP kiyawa na cewar, mun sami labarin cewa wasu matasan unguwar Kurna da Rijiyar lemo suna kokarin afkawa jami’anmu, hakan tasa aka tura karin jami’an tsaro da ke kusa da yankin domin ganin matasan ba su yi nasara ba, kamar ya bayyana hakan a cikin shirin “Dan Sanda Abokin Kowa” na gidan Freedom Radio dake Kano.

SP Kiyawa ya ce yayi mamakin yadda ya gani a dandalin sada zumunta mutane suna ta yada abun da ba haka nan yake ba, musamman kan lamarin da ya faru a unguwar kurna.

Matasan suna so su sami galabar yan sanda ne ta hanyar kona chaji Ofis din da ke unguwar, domin su sami damar cin karensu babu babbaka, ta hanyar shiga shagunan mutane domin yi musu sata”. Inji Kiyawa

Ya ce yanzu haka suna cigaba da gudanar da bincike domin kara samun bayanai sosai don fitowa domin yi wa al’ummar jihar Kano cikakken bayani kan lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *