Zargin Damfara! Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Manajan Bankin FCMB Hukuncin Shekaru 121

Alfijir

Wata babbar kotun jahar Anambra, ta yanke wa wani tsohon manajan Banki hukuncin daurin shekaru 121 a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya,bisa samun sa da laifin karkatar da kudaden abokan huldar banki sama da naira miliyan 112.1m.

Alfijir Labarai ta rawaito hukumar yaki da hana cin hanci da rashawa ta kasa EFCC, ta gurfanar da mutumin tun a ranar 27 ga watan Maris 2018, da tuhume-tuhume 16, da suka hada da Sata, Karya da kuma samar da takaddun bogi.

Wanda ake zargin Nwachukwu Placidus, ya musanta kunshin tuhumar da ake yi masa.

Lauyan hukumar EFCC Mainforce Adaka Ekwu, ya gabatar da shaidu guda hudu ciki kuwa harda wasu takaddu da ya gabatar wa da kotun a matsayin shaida.

Alkalin kotun S. N. Odili ya ce sakamakon samun sa da aikata laifi, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 9 a laifuka guda uku sai kuma daurin shekarun 4 a laifuka 4, shekaru 9 a laifuka 5 da kuuma daurin shekaru 16.

Haka zalika kotun ta umarci wanda aka yanke wa hukuncin ya dawo da kudin abokan huldar da ya karkatar domin bukatar kashin kansa.

Domin Shiga Group

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

One Reply to “Zargin Damfara! Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Manajan Bankin FCMB Hukuncin Shekaru 121”

  1. Wannann hukuncin is out of sense kwata kwata shekara Nawa zaiyi aduniyar sannan wannan hukuncinma talaka Kawai akaraianawa wayo Amma Nanda wadansu watannni zakaji ansakeshi Allah shi kyeuta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *