Ta’addanci! Yan Bindiga Sun Kashe Tare Da Kona Gidan Dagaci Mal Kabiru

Screenshot 20240505 083246 Facebook

Wasu ‘yan bindiga sun kashe Malam Kabiru Mohammed, Dagacin garin Marke da ke unguwar Dandamisa a karamar hukumar Makarfi a jihar Kaduna.

Alfijir labarai ta rawaito ƴan bindigar wadanda ake zargin hayar aka yi ne, sun shiga gidan mamacin ne da misalin karfe 12:30 na daren ranar Alhamis in da suka kori kowa daga harabar gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa sun fara neman Malam Kabiru wanda ke boye a cikin silin tare da kanensa Tukur Mohammed.

A cewar wani dan unguwar da ya nemi a sakaya sunansa, daga bisani ‘yan bindigar sun gano inda dagacin yake, inda suka yanka shi suka kuma banka masa wuta.

Da yake mayar da martani kan lamarin, kansilan unguwar Dandamisa, Alhaji Aminu Sani Marke, ya ce ba a iya gano gawar marigayin ba saboda konewar gidan.

Marigayi Kabiru Muhammad, mai shekaru 30, an nada shi a matsayin Dagacin garin Marke a 2018.

Kokarin Daily Trust na jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna kan lamarin ya ci tura har zuwa lokacin hada rahoton.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *