Zargin fitar da kudade: Jam’iyyar APC ta Gargadi Gwamnatin Kano

FB IMG 1693497487701

Jam’iyyar APC ta koka kan shirin gwamnatin jihar Kano na kashe naira biliyan 8 na kudaden kananan hukumomi ba tare da wani dalili ba.

Alfijir labarai ta rawaito shugaban jam’iyyar APC na jihar n Kano Abdullahi Abbas ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, ranar Talata a Abuja.

Abbas ya bukaci kananan hukumomi da bankunan kasuwanci a jihar da su dakatar da aikin fitar da kudade ga gwamnatin jihar.

Ya ce hakan na faru ne saboda rashin tabbas na siyasa a jihar sakamakon hukuncin kotun koli da ake jira a kan zaben gwamna.

Y Kara da cewa da alama wannan hakan ne ya sa gwamnatin NNPP ta karbe ayyukan kananan hukumomi domin yin almubazzaranci da kudadensu da suka haura Naira biliyan 8.

Ya ce jam’iyyar APC ta samu kwafin takardar amincewa daga ma’aikatar kananan hukumomi ta umurci kananan hukumomi 44 da su fitar da naira miliyan 101 kowannen su domin gina gada a Dan’Agundi da kuma naira miliyan 36 kowannen su don gina wata gadar Tal’udu.

“Wasikar amincewa, wacce aka aika zuwa ga shugabannin kananan hukumomi, an kuma aika da kwafin ta zuwa ga babban mai binciken kudi, masu binciken kudi na kananan hukumomi da dukkanin jami’an ma’aikatar shiyya da suna za ayi musu aiyuka.

Abbas ya ce gwamnatin NNPP ta cire tare da sanya sabbin daraktocin kula da ma’aikata (DPMs) da ma’aji domin cika wannan buri nata, don ganin ba a samu cikas ba wajen murde kananan hukumomin ba ta hanyar almubazzaranci da kudadensu.

Ya yi kira ga gwamnatin jam’iyyar NNPP da ta yi la’akari da muradun al’ummar jihar, inda ya ce matakin gudanar da irin wadannan ayyuka ya fuskanci kalubale tun daga ‘ya’yan jam’iyyar NNPP.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *