Ƴan Sanda Sun Ceto DPO Da Aka Yi Garkuwa Da Shi

Alfijr ta rawaito Rundunar ƴan sanda a jihar Plateau ta samu nasarar ceto DPO din Pankshin, SP Nwapi Augustus, wanda wasu ƴan bindiga su ka yi garkuwa da shi satin daya gabata.

Kakakin rundunar ƴan sandan, Alfred Alabo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a garin Jos.

Alabo, mataimakin Sufeton ‘yan sanda, ya ce biyo bayan sace dan sandan da misalin karfe 8.30 na dare a ranar 11 ga watan Janairu, rundunar, tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro da mafarauta a yankin, su ka kai farmaki, inda a karshe su ka kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane.

“An kai jami’in asibiti domin duba lafiyarsa nan ba da jimawa ba za a sada shi da iyalansa,” in ji sanarwar.

Kakakin ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, Bartholomew Onyeka, ya tura wata tawagar kwararru domin ganin an cafke wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *