Ƴan Sanda Sun Kama Wani Likita Kan Zargin Sacewa Mara Lafiya Koda

Rundunar ‘yan sandan jihar Plateu ta sanar da kama wani likita da laifin sace kodar wata mara lafiya mai suna Kehinde Kamal.

Alfijir Labarai ta rawaito mai Magana da yawun rundunar, DSP Alabo Alfred wanda ya tabbatarwa da manema labarai, ya ce har yanzu ana kan bincike amma tuni wanda ake zargin ya zo hannu.

Kamun na Dr Noah Kekere da ke aiki a asibitin Murma na yankin Yanshanu dake karamar hukumar Jos ta arewa ya zo ne bayan da mijin matar da aka cirewa kodar Alhaji Kamal ya kaiwa ‘yan sanda korafi.

Alhaji Kamal ya zargi Dr Kekere da sacewa matar tasa Ƙoda tun a shekarar 2018.

Da yake yiwa ‘yan sandan karin bayani kan yadda lamarin ya faru, Alhaji Kamal ya ce a shekarar 2018 ne matarsa ta riƙa korafi da ciwon ciki, bayan ya kaita Asibiti ne kuma likitan ya sanar da su cewa tana fama da cutar Appendix, ma’ana tsakuwa ta taru a cikin ta, inda ya bukaci yi mata aiki don fitar da su.

Alhaji Kamal ya ci gaba da cewa “Na biya kudin aiki cikakke, sai dai bayan an yi mata aiki ne kuma sai ciwon yafi na baya tsanani haka muka yi ta fama har tsahon shekara guda kafin muka yanke shawarar komawa gurin Likitan, kasancewar shine ya san matsalar ta amma duk da haka bata daina fama da ciwo ba” a cewar Alhaji Kamal.

Bayan da ya ga ciwo ya ki ci ya ki cinyewa ne kuma ya yanke shawarar kaita asibitin koyarwa na jami’ar Jos, inda aka tabbatar masa da cewa matar bata da Ƙoda daya.

Yace “Da farko ban yarda ba, sai da na kaita wani asibiti mai zaman kansa inda nan ma aka tabbatar min da cewa koda daya ce da ita”.

“Ni abinda nake so kawai ayi min adalci, ina son duniya ta san halin da matata ke ciki”.

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *