Hukumar Kula da ganin wata ta ƙasar Saudiyya, ta sanar da rashin ganin jinjirin watan Shawwal na shakerar 2026 a ƙasar.
Hakan na nufin za a azumci ranar Alhamis 19 ga watan Maris na shekarar 2026 daidai da 30 ga watan Ramadan 1447 bayan Hijra inda a bana za’a gabatar da azumi guda 30 kenan.
Don haka ranar Juma’a 20 ga watan Maris na shekarar 2026 itace ta kasance ranar Sallah karama.
Shafin sada zumunta na Haramain ya rawaito cewa kwarraru masu binciken ganin wata 25 ne suka zauna duba jaririn watan na Shawwal, amma ba’a ganshi ba.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t