Daga Aminu Bala Madobi
Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro (CDS), Christopher Musa, ya bayyana cewa ‘yan Ƙasashen Ƙetare ba za su iya magance kalubalen tsaron Najeriya ba, yana mai jaddada cewa dole ne ‘yan Najeriya su natsu don tabbatar da maido da zaman lafiya.
Musa ya yi wannan jawabi ne ayayin taron al’adun gargajiya da kungiyar hadin kai da kungiyar tsofaffin dalibai ta Unity Schools (USOSANS) ta shirya a Abuja.
Yayin gangamin taron, anyi shagali ba tareda nuna bambancin al’adu ba tare da karfafa manufofin hadin kan kasa.
“Abin da muke gani a yau shi ne yadda Nijeriya ta kasance a dunkule – baki daya ta kowa ce da kowa,” in ji shi.
Musa ya bukaci ‘yan kasa da su yi watsi da rarrabuwar kawuna su koma su hade kai.
“Dole ne mu koyi da zama tare, mu koyi son juna, mu koyi son kasarmu, babu wanda zai iya gyara mana sai mu da kan mu,” in ji shi.
Da yake martani kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na daukar matakin soji a Najeriya, Musa ya ci gaba da cewa alhakin tsaron kasar ya rataya ne kacokan a kan al’ummarta.
“Babu wanda zai ceci kasarmu sai mu da kanmu, dole ne mu yi da kanmu, kuma za mu iya,” in ji shi.
Tun da farko, dayake maida jawabi, shugaban kungiyar ta USOSA, Michael Magaji, ya ce kungiyar ta dukufa wajan kare hadin kan Najeriya da inganta zaman tare.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t