Ƙungiyar Masu Sayar Da Ruwa (Yan Garuwa) Sun Tsunduma Yajin Aiki A Kano

IMG 20240226 115234

Ƙungiyar Masu Sana’ar Garuwa sun tsunduma yajin aikin gargadi na kwana biyu a Jihar Kano, biyo bayan cin zarafi da take musu haƙƙi da suka ce jami’an karɓar haraji na karamar hukumar Ungogo nayi musu a Safiyar Litinin.

Alfijir labarai ta rawaito Ƴan Garuwan sun ce lamarin yana faruwa ne a kan iyakar kananan hukumomin Nasarawa da Ungogo, a titin da aka fi Sani da titin Rimin Keɓe.

Sun bayyana cewa mutanen dake tare su a hanyar na karɓar naira ɗari biyar a hannun su, idan kuma suka gaza biya sai su ƙwace musu Jarakuna ko su ci zarafin su.

Mustafa Ghali ya na cikin ‘Yan Garuwan da suka tafi yajin aikin, ya ce sun ɗauki matakin ne a sakamakon yadda wasu Mutane da basu san ko su waye ba suke tare su suna karɓar naira ɗari biyar a gurinsu, idan kuma basu bayar ba sai su ɗebe musu jarkoki.

Shima Muhammad Shehu Usman ya ce, gani ake kuɗi suke tarawa, bayan ba’a san nawa suke siyan ruwan a gidan ba, ba’a san nawa suke biyan kuɗin kura ba, Kuma ba’a san nawa suke samu ba, adan haka suka tafi yajin aikin domin yanyo hankalin mahukuntan su bincika lamarin.

A nasa bangaren Jikan Malam ya ce, dole ce ta sanya suka tafi yajin aikin domin Al’ummar yankin su gane amfaninsu, tun da suna gani ake cin zarafin su amma kuma sun zuba ido.

A Daren Jiya ne Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Ungogo da Minjibir, Alhaji Sani Adamu Wakili ya dakatar da Karɓar kuɗin harajin naira ɗari biyar ɗin da ma’aikatan Karɓar haraji na karamar hukumar ungogo suke yi, daga hannun ‘yan Garuwan kafin daga bisani kuma wannan sabuwa ta ɓulla a Safiyar Yau.

Matakin zai Shafi Unguwanni Rimin keɓe, Tudun Murtala, Gama dama yankin Birget, Yankunan da suka dogara kacokan akan masu Sana’ar Garuwan duba da yadda suka shekaru masu yawa suna fama da matsalar Rashin Ruwan da suke amfani dashi a dukkan harkokin su na yau da kullum.

GTR HAUSA

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Ahmed Musa

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *