Ƴan Bindiga sun sace mata biyar ciki har da mai shayarwa a Kano

B9

Ƴan bindiga sun kai hari a kauyen Yan Kwada da ke cikin kauyen Faruruwa a Karamar Hukumar Shanono ta Jihar Kano da yammacin jiya Lahadi, inda su ka sace mata biyar, ciki har da masu shayarwa.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Daily Trust cewa maharan sun iso da yawa ɗauke da muggan makamai, inda suka yi wa gidaje da dama dirar mikiya kafin su tafi da waɗanda su ka sace din.

“Sun zo kamar yadda suka saba, suna harbi a iska sannan suna balle ƙofofi suna shiga gidaje. Sun sace mata biyar, ciki har da masu shayarwa” in ji majiyar.

Sai dai, majiyar ta ƙara da cewa mata biyu daga cikin waɗanda aka sace sun dawo, yayin da sauran uku ke hannun masu garkuwa da su har yanzu.

Harin na zuwa ne makonni ƙasa da guda bayan da sojoji suka yi musayar wuta da ‘yan bindiga a yankin, inda aka kashe  19 daga cikinsu.

Rahoton ya ƙara da cewa mazauna yankin Faruruwa da sauran kauyukan kan iyaka tsakanin Kano da Katsina na ci gaba da rayuwa cikin tsoro da fargaba saboda hare-haren ‘yan bindiga da ke maimaituwa a yankin.

Wasu kauyuka da dama kamar yadda Daily Trust ta tabbatar, an bar su babu kowa, yayin da mazaunansu suka tsere zuwa garin Faruruwa ko kuma birane domin neman tsira da kariya.

Daily Nigeria

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *