Theophilus Danjuma, tsohon ministan tsaro, ya bukaci ƴan Najeriya da su dauki nauyin kare kan su a yanayin rashin tsaro da ke addabar ƙasar.
Da yake magana a karamar hukumar Takum ta jihar Taraba, Danjuma ya ce abubuwan da suka faru na sace-sacen mutane da kuma hare-hare na baya-bayan nan sun kara nuna cewa ba za a iya dogaro da gwamnati kadai ba wajen kare ‘yan kasa.
“Na san muna da matsaloli da dama, ciki har da tsaro, kamar kwana biyu ko uku da suka wuce,” in ji shi.
“Mun fuskanci satar mutane kuka barazanar satar mutane za ta ci gaba da kasancewa har sai mun tashi tsaye mu kare kanmu.
“A bayyane ya ke cewa gwamnati ita kadai ba za ta iya ba. Na yi gargadi tun da dadewa, a wani jawabi da na yi a Wukari, cewa dole ne mutanenmu su shirya don kare kansu.
“Wannan gargaɗin ya kasance kamar yau na yi shi.”
The Cable
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD