Ƴan n sanda sun bada rahoton kama Alice Udey, wata mata mai shekaru 33, da ake zargi da satar kayan adon da darajarsu ta kai fiye da dala $60,000 daga wurin mai gidanta kasa da awanni 24 bayan fara aikin ta a matsayin ‘yar aikin gida.
Ana zargin wacce ake tuhuma tana amfani da sunaye na bogi daban-daban, an mika ta ne a ofishin ‘yan sanda na Ikoyi bayan gudanar da bincike na tsawon wata 16.
Rahotanni sun bayyana cewa wacce ake zargin tare da wasu gungun mutane suna kai hari ga gidajen masu arziki.
“Wannan yana kama da wani shiri da aka tsara inda mutane ke kama aikin gida domin su shiga gidaje su sace kayan kudi,” inji wani babban jami’in ‘yan sanda da ya nemi a sakaya sunansa.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj