
Alfijr ta rawaito Gwamnatin Jihar Lagos ta sayo sabbin motoci masu amfani da lantarki don yin aiki da su a matsayin motocin haya.
Gwamnan Jihar, Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.
Ya ce an sayo Motocin ne da zummar saukaka sufuri da rage tasirin sauyin yanayi a Lagos, da ke da mutane fiye da miliyan 15.
Wannan ne karon farko da hukumomi a Nijeriya suka sanar da sayo irin wadannan motoci domin yin sufuri a faɗin ƙasar.

”Sabbin motocinmu masu aiki da lantarki za su inganta sufuri da rage gurbatar muhalli.
Hakan na nufin mazauna birnin Lagos za su daina aiki da fetur su fara amfani da makamashi mai tsafta,” a cewar gwamnan.
Kawo yanzu ba a san adadin motocin bas din da gwamnatin ta saya ba amma Gwamna Sanwo-Olu ya ce za a karo motoci masu yawa da ke aiki da lantarki don inganta sufuri a birnin.

Ya kara da cewa nan da watanni masu zuwa za a soma amfani da motocin a “matakin gwaji.”
A cewarsa hakan zai bai wa gwamnati damar ”tattara isassun bayanai game da aiki da makamashi maras gurbata muhalli” da kuma kwatanta shi da yadda ake aiki da fetur da zummar inganta tsarin sufuri.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ