Gwamnan Kano Ta Amince Da Biya Wa Dalibai Mutum Dubu 7 Kudin Makaranta

Hakan na zuwa ne dai a daidai lokacin da daliban jami’ar ke ci gaba da kokawa da karin kudin da jami’ar ta yi.

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin biya wa daliban da ke karatu a Jami’ar Bayero (BUK) kimanin su subu bakwai 7,000 ’yan asalin Jihar kudin makaranta.

Babban mataimaki ga Gwamnan a kan harkokin kafafen sadarwa na zamani, Salisu Yahaya Hotoro, ne ya tabbatar da haka a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

“Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin biya wa ɗaliban jihar Kano da ke karatu a Jami’ar Bayero su kimanin dubu bakwai kuɗin makaranta,” kamar yadda ya wallafa.

Hakan na zuwa ne dai a daidai lokacin da daliban jami’ar ke ci gaba da kokawa da karin kudin da jami’ar ta yi.

A sakamakon karin, dalibai da dama sun rika neman gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa musu.

Hatta jami’ar ta Bayero sai da ta tsawaita wa’adin lokacin yin rajistar dalibai, kasancewar da dama daga cikinsu ba su iya kammalawa ba, saboda tsadar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *