Kakakin ’yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun shiga farautar wadanda suka aikata wannan mummunar ta’asa.
Alfijir labarai ta rawaito wasu ’yan ta’adda sun kashe wani basaraken gargajiya da wasu ’yan sanda biyu da wani farar hula daya a mararrabar Ahiara da ke yankin Ahiazu na Karamar Hukumar Mbaise da ke Jihar Imo.
Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da sabon kwamishinan ’yan sandan Jihar Imo, Danjuma Aboki, ya soma rangadi tare da jami’ansa a karamar hukumar.
Haka kuma, bayanai sun ce karar kwanan ce ta cimma farar hular wanda tsautsayi ya biyo da shi hanyar, aka yi rashin sa’a harsashi ya same shi.
Shi kuwa basaraken gargajiyar da ya riga mu gidan gaskiya, shigar burtu ’yan ta’addan suka yi tamkar wasu baki masu kawo masa ziyara.
Kakakin ’yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun shiga farautar wadanda suka aikata wannan mummunar ta’asa.
Aminiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp