Gwamnatin Jihar Sokoto ta sauke wasu hakimai 15 bisa zargin su da taimakawa rashin tsaro, kwacen filaye da sauran laifuka.
Alfijir Labarai ta ruwaito an sallami hakimai 9 daga mukamansu bisa zargin su da rashin biyayya da taimakon rashin tsaro da satar filaye da kuma karkatar da dukiyar jamaāa da rashin daāa.
Wadanda aka sallama sun hada da hakiman Uguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tulluwa, llela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu, da kuma Hakimin Gyawa. Gwamnatin jihar ta kuma sauke wasu hakimai shida da tsohuwar gwamnatin jihar ta nada.
Abubakar Bawa, Sakataren yada labarai na Gwamna Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa an sauke hakiman shida ne saboda yadda aka nada su ba bisa kaāida da kuma kin amincewa da mutanensu suka yi.
Hakiman Sun hada da hakimin Marafan Tangaza, Sarkin Gabas Kalambaina, BununGago don ci gaba da bincike.ā
Sai dai Sarkin Yakin Binji, babban mai ba da shawara a Majalisar Suktanate an mayar da shi Nabunkari yayin da Hakimin Sabon Birni ya kai Gatawa.
Bawa ya lura cewa, an bar wasu hakimai bakwai a kan kujerunsu da suka hada da Alhaji Aliyu Abubakar III (Shugaban Sokoto); Alhaji Ibrahim Dauki Maccido (Barayar Zaki); Abubakar Salame (Sarkin Arewan Salame) da Aminu Bello (Sarkin Yamman Balle).
Sauran su ne Mahmoud Yabo (Sarkin Gabas Dandin Mahe); Muntari Tukur Ambarura (Sarkin Gabas Ambarura) da Malam Isa Rarah (Sarkin Gabas Rarah).
Haka zalika, Hakiman Tsaki da Asare suma an rike su yayin da aka mayar da Abdulkadir Mujeli a matsayin Sarkin Rafin Gumbi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai š
https://chat.whatsapp.com/CJ2Q8CMHHOXFY6OEGWV5VK
Amma fa yakamata a gane ma’anar hakimi a Sokoto ba irin ta ba ce, Hakimi a Sokoto shone matsayin Dagachi a Kano wanda muke cewa da shi Hakimi a Kano su kuma suna kiran sa da Uban Kasa