Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani kan korafe-korafen da wasu masu kadarorin da ke kan hanyar BUK suka yi kan sanya musu gine-gine da ma’aikatar filaye da tsare-tsaren jihar ta yi, a ranar 10 ga Yuli, 2024.
Alfijir labarai ta ruwaito masu kadarorin dai sun koka kan matakin da suka bayyana a matsayin wani mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka na rusa ko kuma kwace musu kadarorin.
A rusau din da aka yi a baya a jihar, gine-ginan na daga cikin wadanda aka shirya za a rushe, amma hakan bai yiwuwa ba sakamakon karar da aka shigar da gwamnati.
Sai dai al’amarin na baya-bayan nan ya baiwa masu gine-ginen mamaki inda suka yi kira ga gwamnati da ta duba matakin da take Shirin dauka .
Ibrahim Mu’azzam, wanda yana daya daga cikin masu gine-ginen, ya ce, “Mun tashi ne muka ga wadannan jajayen fenti kamar yadda KNUPDA ta yi a bara. Mun yi iya kokarinmu amma abin ya ci tura daga baya muka kai kara, kuma har yanzu muna gaban kotu.
“Tabbas mun samu wadannan gine-ginen ne a gwamnatin da ta gabata amma wadanda suka mallakesu na asali, sun mallakesu ne kusan shekaru 10 da suka wuce. Duk mutanen da a yanzu suka mallakin wuraren ba su ne wadanda gwamnatin ta basu ba.
“Lokacin da aka sayar mana da wannan wuri ya ma fi hadari, saboda yan daba ne suke cin karensu babu babbaka a wannan wurin, ba irin aiyukan laifin da ba a aikatawa a wannan wurin.
Sai dai da yake mayar da martani game da koken, kwamishinan filaye da tsare-tsare, Abduljabbar Umar, ya ce gwamnati na kan bincike tare da duba yadda aka ba da wuraren kuma za a bayyana sakamakon nan ba da jimawa ba.
“Gaskiyar magana, wurin magudanar ruwa ne kuma akwai rafuka da ganuwa da aka samar tsawon shekarun da suka gabata wadanda suke da tarihi sosai a Kano. Tabbas, mun yi musu alama kuma hakan yana nufin akwai matsala . Ya zama wajibi mu kare tare da tabbatar da cewa an yi komai bisa tsari.
“Mun sami koke-koke daga mazauna yankin game da wanzuwar wadannan gine-ginen da wasu mutane suka gina. Mun bincika kuma mun gani da kanmu.
“Mun shafe shekaru muna fama da matsalolin ambaliya wanda yana daya daga cikin illolin da gine-gine irin waɗannan suke haifarwa. Dukkanmu muna da alhakin kare muhalli, mun yi namu bangaren kuma muna kan bincike kuma nan ba da jimawa ba za mu ga abin da za mu yi.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj