Daga Aminu Bala Madobi
Hukumar EFCC ta tsare shugaban hukumar Hajji ta Kasa, Malam Jalal Arabi da sakataren hukumar Abdullahi Kontagora sakamakon zarginsu da almundahana da naira biliyan casa’in na tallafin kudin aikin hajjin shekara ta 2024.
Alfijir labarai ta ruwaito wasu bayanai da suka bayyana ga ‘yan jaridu, an gano cewa hukumar ta EFCC tayi nasarar karbo riyal dubu dari uku da goma sha hudu da casa’in da takwas daga wadanda ake zargin.
Hukumar tana zargin shugaban hukumar da biyan kansa kudade fiye da abinda doka ta tanadar masa a cikin tallafin naira biliyan casa’in da aka ware domin tallafawa mahajjatan shekara ta 2024.
Sauran Bayanai na nan tafe….
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj