Wata Sabuwar! EFCC Ta Tsare Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa Tare Da Sakataren Hukumar

FB IMG 1723737966402

Daga Aminu Bala Madobi

Hukumar EFCC ta tsare shugaban hukumar Hajji ta Kasa, Malam Jalal Arabi da sakataren hukumar  Abdullahi Kontagora sakamakon zarginsu da almundahana da naira biliyan casa’in na tallafin kudin aikin hajjin shekara ta 2024.

Alfijir labarai ta ruwaito wasu bayanai da suka bayyana ga ‘yan jaridu, an gano cewa hukumar ta EFCC tayi nasarar karbo riyal dubu dari uku da goma sha hudu da casa’in da takwas daga wadanda ake zargin.

Hukumar tana zargin shugaban hukumar da biyan kansa kudade fiye da abinda doka ta tanadar masa a cikin tallafin naira biliyan casa’in da aka ware domin tallafawa mahajjatan shekara ta 2024.

Sauran Bayanai na nan tafe….

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *