Hukumar zabe ta Kano ta kayyade kudin fom ga masu neman kujerar shugabancin kananan hukumomi

B7

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ta kayyade Naira Miliyan goma kudin fom ga masu neman kujerar shugabancin kananan hukumomi.

Alfijir labarai ta ruwaito Shugaban hukumar zabe ta jiha Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya sanar da haka yayin taron manema labarai da ya gudanar a ofishinsa.

Malumfashi yace su kuma masu neman kujerar kansila zasu biya kudin fom naira miliyan biyar kowanne mutum daya.

Hakazalika ya bayyana dokoki da kaidojin zabe, wanda yace dole ne mai neman kujerar shugabancin karamar hukumar kada ya gaza shekaru 30 yayin da mai neman kujerar kansiloli kuma kada ya gaza shekaru 25.

Farfesa ya Kara da cewa dole ne kowane dan takara ya kasance yana da shedar kammala sakandire mafi karanci.

Daga nan ya ja hankalin jam’iyyun da zasu shiga zaben su kiyaye da dokoki da kaidojin hukumar zabe ta jiha.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *