Gwamnatin Kano Ta Bada Umarnin Rufe Dukkanin Asusun Ma’aikatu Da Hukumomin Gwamnati

FB IMG 1723959647845

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin da yake kaddamar da tsarin tattara kudaden haraji da aiwatar da asusun bai daya ajihar Kano wanda hukumar tattara kudaden haraji ta jiha ta aiwatar.

Alfijir Labarai ta rawaito gwamna Abba Kabir wanda ya nuna damuwarsa kan yadda kudaden harajin jihar Kano suke zirarewa ya ce gwamnatin jiha ta aiwatar da tsarin ne domin dakile hanyoyin zirarewar kudi wanda zai bawa gwamnati damar gudanar da ayyukan raya kasa da cigaban al’uma.

Ya ja hankalin shugabannin hukumomi da ma’aikatalun jiha dasu yi biyayya ga sabon tsarin, yana Mai jadda cewa gwamnatin jiha zata dauki matakin ladabtarwa ga duk Wanda suka ki yin biyya ga tsarin.

A nasa bangaren, shugaban hukumar tattara kudaden haraji ta jiha Dr. Zaid Abubakar Yace abin takaici ne yadda jihohin Lagos da River suka yi wa jihar Kano zarra duk da kasancewat cibiyar kasuwanci a kasar nan.

Da yake nasa jawabin, shugaban hukumar yaki ta cin hanci da rashawa ta jihar Kano Barr. Muhyi Magaji Rimin Gado yayi alwashin hukumarsa zata yi kafada da kafada da hukumar tattara haraji ta jiha domin dakile zirarewar kudi da kuma hukumar wadanda aka samu da laifin sace kudaden gwamnati.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *