Kotu ta tsare Ɗan jarida Kan Zargin Caccakar Gwamnan Kano

FB IMG 1723959647845

Wata kotun majistare da ke Kano ta tsare Muktar Dahiru, dan jarida, bisa zarginsa da yin wani rubutu da ya wallafa a Facebook, inda aka yi la’akari da cewa ya ci mutuncin Abba Yusuf, Gwamnan jihar.

Alfijir Labarai ta rawaito ranar Alhamis ne aka kama Dahiru wanda ke aiki da gidan rediyon Pyramid FM Kano da ke karkashin gidan rediyon tarayyar Najeriya (FRCN).

A cewar Premium Times, an gurfanar da dan jaridar a asirce a gaban kotun majistare 24 da ke Gyadi Gyadi, titin kotu, da laifin hada baki, bata sunan mutum, da kuma batanci da gangan.

Alkalin kotun, Ummah Kurawa, ta tasa keyar Dahiru a gidan gyaran hali, har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron karar neman belin ranar 3 ga watan Satumba.

An ce dan jaridar ya yi hira da wani dan siyasan adawa a wata hira da aka watsa a cikin sautin murya yana zargin gwamnan da cin hanci da rashawa.

Dan siyasar na adawa ya bukaci gwamnan da ya baiwa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na tarayya damar gudanar da bincike kan badakalar Novomed maimakon hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACAC).

A kwanakin baya ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da badakalar sayen magani na biliyoyin naira.

Cikin wadanda aka kama har da Garba Kwankwaso, kane ga Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano.

Garba shine manajan darakta na Novomed Pharmaceuticals.

Garba da wasu jami’ai an zargi su da karya dokokin sayo kayayyakin gwamnati ta hanyar hada baki da Novomed kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomin a cikin sanarwar.

An kuma ce dan jaridar ya wallafa wani shirin faifan sauti wanda a cikinsa wani mutum ya zargi Muhammadu Sanusi, Sarkin Kano da aka dawo da shi, da nuna kansa a matsayin mai tausaya wa talakawa yayin da yake rayuwa mai tsada A bayan fage.

Ya kuma raba wani faifan faifan murya na Yusuf Fasaha, dan siyasar adawa, yana zargin Kwankwaso da zamba.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *