Buwayi Gagara Misali! Wata Akuya Ta Haifi Awaki Siffar Mutane A Kano

Hoto Alfijir Labarai

Daga Aminu Bala Madobi

Wanda yayi unguwar zomancin akuyar lokacin da yazo zaro ‘ya’yan awakin, fita yayi aguje sakamakon ganin abinda bai saba gani ba.

Alfijir Labarai ta rawaito wata akuya a mayankar Tudun Wada da ke yankin karamar hukumar Nasarawa a Kano ta haifi ‘ya’yanta biyu da sukai suffar kamannin dan Adam.

Hakan na zuwane sakamakon haihuwa da akuyar tayi a jiya Alhamis da yamma amma sai dai kuma akuyar tasha doguwar nakuda, lamarin da ya saka akayi hanzarin yankata bisa ganin zata iya kasawa sakamakon laulayin da take fama dashi.

Rahotanni sunce ana zargin ko dai wani mutum a baya ne yayi tarayya da akuyar don biyan wata bukatar shi, wasu kuma na ganin abu ne kawai daga Allah.

Mamallakin akuyar a tattaunawar wakilin Alfijir da shi, ya bayyana cewa gani yayi akuyar najin jiki matuka, nan take ya garzaya da ita asibitin su dake mayankar, walaa Allah tayi rai, idan kuma aka ga baza takaiba ayanka.

Wasu Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an kawo akuyar a lokacin da take tsaka da nakuda, kuma a gaggauce aka ga ba zata iya haihuwa ba nan take akayi mata ofreshon domin ciro yayan masu siffar mutane.

Shima Sarki mayankar dabbobin dake kasuwar Tudun Wada Abdulmumin Dauda ya ce tabbas akwai cincirindon kwankwamai da abubuwan ban tsoro tattare cikin manyankar.

Sarkin ya tabbatar da cewa wanda yayi unguwar zomancin akuyar lokacin da yazo zaro ‘ya’yan awakin, fita yayi aguje sakamakon ganin abinda bai saba gani ba.

Buwayi gagara misali.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *