Karin kudin man dai yasa ana siyar da lita daya daga Naira 897 a gidajen man NNPC, maimakon 617 da ake siyarwa a baya, a gidajen man ‘yan kasuwa ake siyar da duk Lita 980 zuwa 1, 200.
Alfijir Labarai ta rawaito sa yake bayani yayin ganawa da ‘yan Nijeriya a birnin Beijing na China, Tinubu ya ce karin kudin man “Mataki ne mai tsauri wanda ba a saba gani ba” da ya zama dole don ci gaban Nijeriya.
A sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ambato shi na cewa matakan da gwamnatinsa ke dauka na daga cikin dabarun dora tattalin arzikin Nijeriya bisa turba.
Sai dai al’ummar Nigeria na ci gaba da kokawa da sabbin manufofin shugaban ƙasar, wadanda suka sanya ƙasar cikin mawuyacin.
Tinubu ya ce nan ba da jimawa yan Nigeriya zasu Fara amfana da sabbin manufofin da aka fito da su don inganta tattalin arzikin kasar.
Domin haka kowa ya kara hakuri da juriya, canji na nan zuwa.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj.