Mai magana da yawun shugaban kasa Bola Tinubu, na Najeriya Chief Ajuri Ngelale ya ajiye aiki sakamakon rashin lafiya.
Alfijir Labarai ta rawaito Ajuri, ya bayyana hakan ne a wata takaitacciyar sanarwa da ya fitar a yau Asabar.
“A ranar Juma’a, na mika takarda ga shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, inda na ke shaida masa cewa na tafi hutu na sai-baba-ta-gani domin mayar da hankali kan batun rashin lafiya wanda hakan abun damuwa ne ga ahali na.
” A yayin da na ke godiya kan wannan nauyi da aka dora min wanda yanzu ya kai matakin yanke shawarar dakatawa da aikina a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin yada labarai, kuma mai magana da yawunsa; jakada na musaaman ga shugaban kasa a fannin sauyin yanayi kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan shirin Evergreen.
“Na dau wannan matakin ne bayan tuntubar iyalina a yayin da rashin lafiya ya tsananta a gida na.
Zan dawo bakin aiki da zarar waraka ta samu kuma lokaci ya bada dama,” in ji Ngelale.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj