Ana Wata! Sama Da Fursunoni 200 Ne Suka Tsere Daga Gidan Gyaran Hali A Maiduguri

IMG 20240910 WA0218

Sama da fursunoni 200 sun tsere daga gidan yarin birnin Maiduguri da ke jihar Bornon  Najeriya bayan ambaliyar ruwa ta rusa katangar gidan yarin.

Alfijir Labarai ta rawaito Ɗaya daga cikin jami’an da ke tsaren gidan gyaran hali da ya buƙaci a sakaya sunansa, shi ne ya tabbatar wa da RFI Hausa cewa, fursunonin sun yi amfani da damar ibtila’in ambaliyar wajen tserewa.

Kazalika jami’in ya bayyana cewa, akwai mayaƙan Boko Haram da ake tsare da su a wannan gidan yarin na New Prison, kuma wasu daga cikinsu sun arce.

A ɓangare guda, akwai wasu fursunoni sama da 200 na daban da su kuma aka sauya musu gidan yari kamar yadda jami’in ya yi ƙarin haske.

Ambaliyar ta kuma rusa ɗakunan jami’an da ke tsaren gidan yarin.

Wannan na zuwa ne a yayin da al’ummar jihar Borno ke cikin zullumi biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye yankuna da dama a cikin tsakar dare.

Ya zuwa yanzu babu wani bayani a hukumance game da irin mummunar asarar da aka tafka a sakamakon ambaliyar ruwan wadda ta mamaye dubban gidaje da hanyoyi.

RFI Hausa

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *