Tarihi! Makabartar Fadar Gidan Rumfa a Kano Na Dauke da Sarakuna Fiye da Makabartar Gidan Nassarawa

Fadar kano 1

   – Daidai lokacin da Sarki Aminu Ado Bayero ke gyaran fadar Nasarawa

Wani bincike na musamman ya nuna cewar a Makabartar dake Fadar Gidan Rumfa an binne dukkan Sarakunan Habe tun daga kan Muhammadu Rumfa har zuwa Sarakunan Fulani irin su Sarki Sulaiman da  Sarki Ibrahim Dabo da Sarki Muhammad Bello da Sarki Usman.

A Makabartar dai an binne mutane sama da guda Dari (100), tun daga kan Sarki Muhammadu Rumfa zuwa Sarki Usman tare da matan duka Sarakunan. Hatta mahaifiyar Sarki Ibrahim Dabo da Sarki Muhammadu Sanusi I (na daya) da kuma Kakar Muhammadu Sanusi II (na biyu) wato Uwar Soro Wayo, duk a Makabartar Gidan Rumfa a ka binne su.

Sabanin Makabartar Gidan Nassarawa wacce take dauke da Sarakuna guda biyar. Wato Sarki Abbas, Sarki Abdullahi Bayero, Sarki Muhammad Inuwa, Sarki Muhammadu Sanusi I da kuma Sarki Ado Bayero.

A tarihin masarautar Kano, Makabartar Gidan Rumfa wacce ke dauke da manyan mutane sama da Dari, ita ce Makabartar farko ta Sarakunan Kano. Amma Makabartar Gidan Nassarawa daga lokacin Sarki Abbas a ka samar da ita.

Domin inganta makwancin manyan kasa shugabannin al’umma, lokacin da a ka nada Aminu Ado Bayero Sarkin Kano, ya gyara babbar Makabartar ta Gidan Rumfa.

Yanzu haka kuma ya na gyaran Makabartar Gidan Nassarawa, wacce yanzu haka za ta iya daukar mutane sama da Ashirin. Maimakon iyakacin mutane Biyar.

Ba a nan kawai ya tsaya ba, Mai Martaba Sarki Aminu Ado Bayero, kamar yadda ya gyara Soron Ingila lokacin da ya tarar da Soron tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I ya mayar da shi wajen wanka (swimming pool) da shakatawa, amma Sarki Aminun ya na zama Sarkin Kano, ya sa a ka dawo da shi matsayin sa na Soron Ingila.

To haka ya tsaya ka’in da na’in ganin cewa Fadar Nassarawa ma ta samu gyara mai kyau da zai dace da dukkanin wata Fada mai Alfarma. Wanda tuni an ma fara yin wasu abubuwa tun daga Makabartar da take cikin Fadar.

A wancan lokacin da Mai Martaba Aminu Ado Bayero ya yi wancan gyaran na Soron Ingila akwai a kokarin sa na gyara babbar Makabartar ta Gidan Rumfa, daidaikun mutane da kamfanoni sun taka rawar gani wajen aiwatar da gyaran.

Yanzu haka ma tuni har irin wadannan masu kokarin sun fara nuna sha’awarsu na gyaran ita Fadar Gidan Nassarawa. A yanzu haka ma magana ta yi nisa cikin taimakon Allah. Dan kuwa har an fara yin wasu gyare-gyaren.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *