Takaddama Kan Farashin Fetur Ta Kaure Tsakanin NNPC Da Matatar Dangote

Dangote

A wata sanarwa da kamfanin Dangote ya fitar ya ce ya sayarwa da kamfanin NNPCL da man fetur din da kudin dalar Amurka ba da Naira ba.

Alfijir Labarai ta rawaito ricikin farashin man fetur ya barke tsakanin Kamfanin NNPCL da kamfanin Dangote bayan da NNPLC ya ce ya sayi kowace lita a kan Naira 898, farashin da kamfanin Dangote ya ce ba gaskiya ba ne.

A wata sanarwa da kamfanin Dangote ya fitar ya ce ya sayarwar da kamfanin NNPCL da man fetur din da kudin dalar Amurka ba da Naira ba.

Wannan ya nuna cewa farashin man a gidajen mai ba zai gaza Naira 900 ba ke nan, ko da kuwa a birnin Legas ne mai abin hawa zai sayi man.

Da yake tsokacin kan ko ta yaya samar da man a cikin gida zai taimakawa tattalin arzikin Najeriya, Dakta Dauda Mohammed Kontagora, masanin tattalin arziki ne da saka jari a Najeriya, ya ce wannan abin yabawa ne, sai dai babu sauki ga ‘yan kasa, tun da NNPCL ta gaje kasuwar a yanzu.

Kamfanin NNPCL, wanda ke da matatun man fetur 4 da Depot-Depot a jihohin kasar da dama, ya kasa sarrafawa da rarraba man fetur a cikin shekaru fiye da 25.

Kamfanin NNPCL yana sayo man da yake sayarwa daga danyen mai a kasashen waje, abin da kuma ke haifar da asara da tsadar mai a cikin gida.

Sai dai yanzu haka kamfanin man na Dangote ya musanta bayanan da NNPCL ya fitar da ke cewa ta sayi man ne a kan kudi Naira 898 a kan kowace lita.

Kamfanin Dangote duk da cewar bai fadi farashin da ya sayar wa da NNPCL ba, ya ce ya sayar masa ne da kudin dalar Amurka kuma kasa da yadda NNPCL ta saba sayowa a kasashen waje.

Fassarar VOA

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *