Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kyakkyawan tsari na haihuwa kyauta a dukkan Manyan asibitocin jihar Kano.
Wannan wani babban abin alfahari ne na Jin dadi domin zai taimaka wajen ragewa mutane radadi a lokacin haihuwa.
A wannan lokacin an Samar da tsari me kyau na tabbatar da cewar duk macen da ta haihu a daya daga cikin wadannan asibitoci to ba‘a bukatar ko sisin kobo daga gare ta ko ‘yan uwan ta.
Abin Farin ciki ne yadda aka yiwa tsarin tanadi na musamman yadda babu wata hanya da za‘a ce Kayan ya kare.
Kowanne asibiti dake matakin Sakandare fasiliti (Ban da asibitin Nasarawa) yana cikin wannan tsari, kuma gwamnati tana bayar da isassun Kaya na haihuwa a dukkan asibitocin.
Dan haka duk sanda ka je haihuwa a wadannan asibitocin babu batun biyan kudin haihuwa ko sayen wani abu komai kyauta ne.
Idan an bukaci ka biya kudi to ka sanar da hukumar asibitin ko hukumar lura da asibitocin jihar Kano.
Allah ya kara yin riko da hannun shugabannin mu wajen sauke nauyin dake kan su. Muma Allah ya bamu kwarin gwiwar haska musu a inda suke bukatar gyara da karfafa musu gwiwa Idan sun yi daidai.
Allah ya albarkaci Kano da Nigeria



Nasiru Zango
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj