Gwamnatin Najeriya Ta Amince Da Kaddamar Da Wasu Muhimman Ayyuka A Zaman Majalisar Zartarwa

Screenshot 20240819 123738 Facebook

Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da aikin gina tituna 14 da gadoji wanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Ekiti da Adamawa da Kebbi da jihar Enugu.

Alfijir Labarai ta rawaito ministan ayyukan, David Umahi ne ya bayyana hakan yayin yiwa manema labarai na fadar shugaban kasa bayani bayan zaman majalisar zartarwar.

Ya ce sauran jihohin sun hada sa Cross River da Ondo da jihar Osun da Ebonyi da Abia da jihar Imo.

Ya ce, an bada aikin kwangilar gina hanyoyin ne kari kan kwangilar gyara gadar Gamboru dake Gamboru-Ngala da Kala-Balge a jihar Borno.

Minsitan ya ce majalisar ta kuma amince da sabuwar kwangilar gina hanyar Maraban-Kankara da Funtua a jihar Katsina.

Haka kuma, majalisar ministocin karkashin jagorancin shugaba Tinubu ta amince da gina hanyar Afikpo zuwa Uturu-Okigwe a jihar Ebonyi da Abia da jihar Imo.

“Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fitar da Naira Biliyan 80 don kammala wannan aikin, wanda jimilla ya kama biliyan 280.”

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *