Da Dumi Duminsa: NNPP ta dakatar Da Sakataren Gwamnatin Kano da kwamishinan sufuri

FB IMG 1723959647845

Daga Aminu Bala Madobi

Jam’iyyar NNPP ta dakatar da sakataren gwamnatin jihar Kano, Dakta Abdullahi Baffa Bichi, da kwamishinan ma’aikatar sufuri, Muhammad Diggol

Alfijir labarai ta rawaito shugaban jam’iyyar na jihar, Hashimu Sulaiman Dungurawa ne ya sanar da hakan a yammacin ranar Litinin.

A cewar Dungurawa, dakatarwar ta biyo bayan korafe-korafe da dama daga shugabannin mazabu da na kananan hukumomi na jam’iyyar.

Shugaban ya ce an dakatar da su ne saboda rashin mutunta jam’iyyar da shugabancin ta.

“Jam’iyyar ba za ta lamunci ayyukan da ke lalata shugabancinta da tsarinta ba. Bayan mun samu korafe-korafe daga mazabun  su, da kuma tabbatar da zargin da shugabannin yankin suka yi mana, ba mu da wani zabi illa daukar wannan muhimmin mataki,” in ji Dungurawa.

Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano ta Arewa a karkashin shugabancin Sulaiman Dambatta, ya kara tabbatar da wannan zargi, wanda ya kai ga yanke hukuncin dakatar da jami’an guda biyu.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa dakatarwar ta zo ne ‘yan mintuna kadan bayan da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sasanta Baffa Bichi da dan takarar shugaban karamar hukumar Bichi Hamza Sule Maifata.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *