Rana Dubu! An kama wani Ɗan sandan bogia Kano

Police

Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta kama wani Dan Sandan Sarauniya na bogi, mai suna Salisu Bala , mai Shekaru 31 mazaunin unguwar Kurna.

Alfijir labarai ta rawaito an kama wanda ske zargin a ranar 14 ga watan Oktoba 2024, bayan samun rahotanni daga unguwanni, Sabon Gari da Fagge da Koki da sauran su unguwanni akan cewar wadansu batagari suna fitowa a matsayin Yan Sandan Kwansitabulare suna cutar mutane.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aike wa da manema labarai.

Sanarwar ta ce bayan Samun rahotanni kwamishinan yan Sandan jahar Kano  Salman Dogo Garba, yace Yan Sanda da suke Aiki a yankunan , su Sanya ido da fadada Sintiri duk inda aka ga irin wadannan batagari akamo su.

Yan Sandan Sarauniya ne suka kama wadanda ake Zargin saboda bata mu su suna da yake Yi.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kara da cewa an dawo da shi sashin binciken manyan laifuka dake  Rundunar Yan Sandan Kano a unguwar Bompai.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *