Daga Aminu Bala Madobi
Hukumar Hisbah ta kama wani kwamishinan jihar Jigawa bisa zargin sa da lalata da matar aure a Jihar Kano.
Alfijir labarai ta rawaito kwamishinan da hukumar ba ta bayyana sunansa ba, ya shiga hannu ne bayan ƙarar da mijin matar ya shigar, inda yake zargin matar kuma uwar ’ya’yansa biyu tana lalata da kwamishinan a bayan idonsa.
Wani jami’in hukumar da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa Aminiya cewa sun kama kwamishinan da matar ne bayan jami’an Hisbar da mijin matar sun rutsa su a wani kango mallakin kwamishinan a cikin mota.
Ya ce, ganin su ke da wuya, matar ta yi yunƙurin tserewa a motar, inda ta buge mai gadin.
Amma ya bayyana cewa daga bisani rundunar ta samu nasarar tsayar da ita da nasu motocin.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj