Gwamnatin Najeriya ta karbo wani sabon bashi daga bankin raya kasashen Afrika da ya kai na dala miliyan 134, domin a taimakawa manoma wajen bunkasa sha`anin samar da irin shuka da kuma habaka noman abinci a kasa baki daya.
Alfijir labarai ta rawaito ministan ma`aikatar gona da bunkasa samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis 14 ga wata a Calabar ta jihar Cross Rivers yayin bikin kaddamar da shirin noman rani na shekara ta 2024 zuwa 2025.
Ministan gonar ya ci gaba da cewa sakamakon bullo da shirin noman rani na kasa wanda ke da nufin yin noma babu kakkautawa a dukkan tsawon shekara, babu shakka bashin da aka ciwo zai kara bayar da kwarin gwiwa na kokarin da ake yi na wadata kasa da abinci.
Sanata Abubakar Kyari ya ce da ma dai tun a baya gwamnatin tarayya ta daura damarar gangamin noman abinci domin tabbatar da ganin kowanne dan Najeriya yana da ikon samun abinci mai gina jiki kuma cikin rahusa.
Ya kara da cewa gwamnati tana son ta yi amfani da bangaren noma wajen farfado da tattalin arzikin kasa, ta hanyar mayar da hankali sosai wajen kara adadin noman wasu nau`ikan kayan abinci, kamar Alkama da Shinkafa da Masara da Dawa da Waken suya da kuma Rogo a lokutan noman rani da na damuna.
Ministan gonar na tarayyar Najeriya ya ce a kwanan nan gwamnati ta agazawa manoma kusan dubu 193 a karkashin shirin noman damuna na shekara ta 2024 a jahohi 37 ciki har da Abuja.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj