Wani mai maganin gargajiya mai suna Ismail Usman ya samu raunin harbin bindiga yayin da yake gwada laya mai kare harbi a unguwar Kuchibiyi, karamar hukumar Bwari, a Birnin Tarayya, Abuja.
Alfijir Labarai ta rawaito wani mazaunin Kuchibiyi, Samson Ayuba, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, lokacin da mutumin, a kokarinsa na gwada tasirin layarsa mai kare harbi, ya harbi kansa a ciki.
Ya bayyana cewa mai maganin ya yanke jiki ya fadi nan take, sannan wasu maƙwabta suka yi gaggawar daukar sa zuwa asibiti.
“Mutumin bokane, yana hada magunguna da layoyi na gargajiya. A ranar Alhamis, ya yi kokarin gwada bindiga a kan kansa bayan ya sanya laya mai kare harbi, amma layan ya kasa kare shi,” in ji shi.
Yayin tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yansandan FCT, SP Adeh Josephine, ta ce wanda abin ya faru da shi ya yi amfani da bindigar gargajiya ya harbi kansa a ciki.
Ta ce jami’an ‘yansanda daga sashen Byazhin sun yi gaggawar kai dauki inda suka tarar da wanda abin ya shafa cikin mawuyacin hali.
Ta ce bayan kai shi asibiti, ƴansanda sun bincika dakin mutumin inda su ka samu bindiga kirar gida da kuma layoyi da guraye.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj