Rundunar yan sandan jihar Katsina ta kama wani jami’in banki a Daura bisa zargin sace N18m daga asusun wani abokin huldar bankin ta hanyar na’urar ATM.
Alfijir Labarai ta rawaito wanda ake zargin, shi ne mataimakin jami’in ayyuka a wani banki, an zarge shi da hada baki da abokansa domin aikata laifin.
ASP Abubakar Aliyu, kakakin rundunar yan sandan Katsina, ya tabbatar da kamen yayin wani taron manema labarai a hedikwatar yan sandan jihar Katsina ranar Alhamis.
ASP Aliyu ya bayyana cewa an fara bincike kan batun ne bayan da wanda abin ya shafa, Okojie Herbert, ya kai rahoton abin da ya faru.
“Bayan samun korafi daga Okojie Hubert Erayomon, mazaunin Daura, wanda ke matsayin mataimakin shugaban ayyuka a Access Bank, reshen Daura, kan zargin almundahanar da aka yi wa Adewumi Bolaji Gabriel, mai shekara 28, shugaban ATM na bankin Access reshen Daura, Jihar Katsina, an gano cewa wanda ake zargin ya haɗa baki da abokinsa, David Mesioye, ma’aikacin Access Bank reshen Kafur, wanda yanzu haka ya tsere, domin sace naira miliyan goma sha takwas da dubu dari ɗaya da sittin da huɗu (₦18,164,000.00) daga asusun wani abokin huldar banki.”
Ya kara da cewa jami’an tsaro suna nan suna neman abokin wanda ake zargin da ya tsere don gurfanar da shi gaban kuliya.
Gwamna Yusuf ya ziyarci ɗaliban Kano da ke kan tallafin karatu a Indiya
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yabawa kyakkyawan nasarar ilmantarwa da ɗaliban da gwamnati ta dauki nauyin su don ci gaba da karatu a Indiya. A Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yabawa kyakkyawan nasarar ilmantarwa da ɗaliban da gwamnati ta dauki nauyin su don ci gaba
Daily Post
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj