Ko ana muzuru ko ana shaho Najeriya zata kai ga nasara – in ji Tinubu

FB IMG 1723115651747

Shugaba Bola Tinubu ya ce al’amura suna tafiya yadda ya kamata, duk da mutane ba sa son gwamnatinsa.

Ya ce a cikin kalubalen da kasar nan ke fama da shi, gwamnatinsa ta samar da ci gaba, inda ya ce anan gaba za’a ci gajiyar sauyin daya kawo.

Shugaban wanda ya samu wakilcin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana hakan a wajen bikin yaye daliban Cibiyar Nazarin Tsaro ta kasa da ke Abuja, ranar Asabar.

Ya ce, “Abubuwa suna faruwa a kasarmu a yau. Wataƙila mutane ba sa son mu. Wataƙila suna kin jinin manufofinmu, amman duk da wannan abubuwa suna canzawa kuma Najeriya za ta canza.”

Tinubu ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya kudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar.

Ya ce mutanen da ke aikata laifi za su fuskanci shari’a ba tare da la’akari da inda suke zaune ba. “ ko kana cikin Najeriya ko a waje ka aikata laifi za mu bibiye ka mu gurfanar da kai a gaban kuliya,” inji shi

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *