Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi mai tsanani game da satar kudaden da aka ware wa kananan hukumomi, tana mai cewa wannan na daga cikin laifukan da za a iya tuhumawa.
Alfijir Labarai ta rawaito wannan gargaɗin na zuwa ne bayan wani hukunci na Babban Kotun Najeriya da ya ba da ‘yancin kudi ga dukkan kananan hukumomi 774 a Najeriya.
A yayin taron shekara na kungiyar ‘Yan Jarida na Shari’a ta Abuja (NAJUC) na 2024, Ministan Shari’a da Babban Lauya na Ƙasa, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya jaddada kudirin gwamnatin Tarayya na gurfanar da duk wani jami’in da yayi amfani da kudaden kananan hukumomi biaa ka’ida ba.
Fagbemi ya bayyana damuwa game da yadda gwamnonin jihohi ke amfani da tsarin kananan hukumomi wajen saka mabiya su ta hanyar zabe da ba a yi da gaskiya ba.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj